Zaben 2023: Za a iya hasashen Zaben badi a yankin arewa maso yamma-Tambuwal

Aminu Tambuwal 750x430 1
Aminu Tambuwal 750x430 1

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi hasashen cewa shiyyar arewa maso yammacin kasar za ta iya hararo sakamakon zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa idan aka yi la’akari da yawan masu kada kuri’a a shiyyar.

Gwamnan ya kuma ce, tunda babu wani dan takarar shugaban kasa mai kwari daga shiyyar, manyan jam’iyyun biyu sun kuduri aniyar yin kamfen sosai a yankin.

Ya bayyana haka ne a Sokoto lokacin da shugabancin riko na wata kungiyar magoya bayan Atiku na PDP Mai suna ‘Atiku United Front’ ta kai masa ziyara.

Gwamna Tambuwal ya ce jam’iyyar PDP za ta tallafa wa irin wadannan kungiyoyi a shiyyar domin bunkasa karfin jam’iyyar.

Tambuwal ya ce, yankin ya sha fama da matsalar ta’addanci fiye da sauran yankuna a kwanakin baya.

Ya yi alkawarin cewa PDP za ta magance matsalar rashin tsaro a kasar nan kamar yadda aka bayyana a cikin ajandar yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubakar.

Gwamnan ya kuma ce ya ji dadin jin cewa kungiyar za ta yi wa dukkan ‘yan takarar jam’iyyar aiki.

Kazalika ya bayyana godiyarsa ga Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa bisa kokarin da ya yi wajen kafa kungiyar.

Tun da farko Darakta Janar na kungiyar Malam Shehu Kura ya ce sun yanke shawarar ziyartar gwamnan ne domin fahimtar da shi manufar kungiyar saboda matsayinsa na shugabancin jam’iyyar a shiyyar.

Malam Shehu Kura ya ce a matsayinta na jam’iyyar PDP za ta yi kokarin tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan matakai a shiyyar.

Ya ce kasancewar shi kadai ne gwamnan PDP a shiyyar, suna ganin shi ne zai fara karbar kungiyar.

Ya kuma yabawa gwamnan bisa kishin kasa da kuma hangen nesa wajen sauka daga mukaminsa na wanda ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa domin ceto jam’iyyar da Kuma dimokuradiyya a kasar nan.

Malam Shehu ya bayyana irin wannan yanke shawarar na rashin son kai a matsayin abinda yawancin ‘yan siyasar kasar nan basu da shi.

Shima da yake nasa jawabin shugaban kungiyar Alhaji Umar Danjani Hadejia ya godewa gwamnan bisa karbar kungiyar tare da tabbatarwa gwamnan cewa da yardar Allah nasara ta jam’iyyar PDP ce a zabubbukan dukkan matakai na shiyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here