Shugaba Buhari ya bawa Tinubu tutar takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC

images 4 1 750x351 1
images 4 1 750x351 1

Shugaban kasa Muhammadu Bahari ya mikawa Asiwaju Bola Tinubu tutar takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, bayan kammala zaben fitar da gwani da aka kammalashi a yau Laraba.

Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya ya rawaitu cewa daliget din APC sun zabe tsohon gwamnan Jihar Legas a matsayin wanda zai yi takara a kakar zaben 2023.

Tinubu ya sami karu’u 1,271 wanda ya bashi damar kayar da tsohon ministan sifiri, Rotimi Ameachi da yazo na biyu a zaben, Ameachi ya sami kuri’u 316, yayin da Osinbajo  ya sami kari’a 235

Yayin da yake karbar tutar, Tinubu ya godewa shugaban kasa Buhari, shugaban jam’iyyar ta APC, gwamnonin APC, daliget da kuma abokanan da suka kara dashi ya yin zaben. Sannan kuma ya nema a bashi hadin kai domin a kai ga samun nasarar cin zaben 2023.

 

 

 

 

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here