Bola Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a  jam’iyyar APC

Tinubu speaking
Tinubu speaking

Bola Ahamad Tinubu Ya lashe zaɓen ne da ƙuri’a 1,271, a zaben-fitar da gwani na jam’iyyar APC.

Sakamakon zaben da aka baiyana ya nuna cewa, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri’a 316, yayin da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sami ƙuri’u 235.

Sai Shugaban majalisar dattije Sanata Ahmad Lawan ya samu ƙuri’u152.

Ya yin da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu ƙuri’a 47, sai tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha wanda bai samu ƙuri’a daya ba

 Gwamnan jihar Cross River Ben Ayade ya samu ƙuri’u 37, gwamnan Ebonyi Dave Umahi ya samu ƙuri’u 38, sai tsohon gwamnan Zamfara Ahmad Sani Yariman Bakura ya samu ƙuri’u 4

Yan takara 7 ne suka janyewa Bola Ahamad Tinubu

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here