Majalisar dokokin jihar kano ta aminciwa  gwamna Ganduje ya ciyo bashin naira biliyan 10

Ganduje Speaking Green 2
Ganduje Speaking Green 2

Majalisar dokokin jihar Kano ta amincewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ciyo bashin naira biliyan 10.

A zaman ta na yau Laraba, shugaban majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta wasikar mai kwanan wata 10 ga watan March 2022, da Ganduje ya tura mata, don  neman sahale masa ya ciyo bashin naira miliyan 10.

Bayan ya gama karanta takardar, ‘yan majalisar sun amunci da bukatar, bayan shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdul Madari, wanda shine yake wakiltar Warawa da kuma Ayuba Labaran, mai wakiltar Kabo, sun marawa bukatar sahaliwar baya.

Ta cikin wasikar da ya aike majalisar, gwamna Ganduje ya ce manufofin ceyo bashin shine, a samar da na’urorin tsaro na zamani CCTV, a cikin birnin Kano da kuma masarautu biyar da muke dasu a jihar Kano.

Ya kara dewa bukatar hakan yazama dole, don maganci barazanar tsaro da jihar Kano ke fuskanta a halin yanzu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here