Mutum tara sun mutu, yayin da wasu goma suka samu raunuka a wani mummunan hadarin mota da ya auku a yankin Yangoji-Abaji da ke Abuja babban birnin Najeriya
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kiyaye hadura ta Najeriya FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Kamfanin dillacin labaran kasar NAN ya ambato mista Kazeem na cewa hadarin ya auku ne jiya da safe.
Ya kara da cewa motar daukar fasinjan wadda ta taso daga Osun zuwa Katsina ta yi karo da motar daukar kaya.
Sanarwar ta ce ”Lamarin ya rutsa da mutum 22, kuma dukkansu maza ne, goma sun samu raunuka, yayinda tara suka mutu”.