Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama mutum takwas a wani kungurmin daji da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a dajin jihar Ondo.
An kuma samu abubuwa masu fashewa da bindiggi da harsasai da kuma tabar wiwi.
Wakilin BBc ya ruwaito cewa lamarin na zuwa ne a lokacin da hukumar ta kama wani mutum dan shekara 53 mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel da kwayar Tramadol a zauren a filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake a Legas.
A sanarwar da Femi Babafemi ya aike wa manema labarai ya ce jami’an hukumar ta NDLEA sun kaddamar da samamen ne bayan wani rahoto da aka tsegunta musu, sai suka fantsama cikin kungurmin dajin Ala da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, inda suka kama mutum takwas.d
An kama wadanda ake zargin ‘yan fashin ne a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da buhu 25 na ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 296, da wasu abubuwa masu fashewa kamar bom guda shida da harsashin bindiga shida.
Akwai kuma babura guda hudu da layu daban daban da suke amfani da su wajen aikata ta’addanci kan mutane da suka sha tsarewa a dajin.
Wannan na zuwa ne a lokacin da jami’an suka kama wasu mutane masu sarrafa hodar Ibilis da ake kira Metanpethamine a Agbara dake a wajen birnin Legas.
Kamen hodar methanpethamin ya zo a lokacin da jami’an hukumar suka sake kama wani mutum mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel a zauren masu shirin tafiya a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a Legas bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi nau’in Tramadol kimanin kwali dubu biyar da ya boye a cikin jakarsa.













































