Kungiyar Buhari Media Organisation BMO ta caccaki tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kan ikirarin da yayi na cewa bangaren shari’a da na majalisa suna karkashin ikon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Niyi Akinsiju da sakatarenta Cassidy Madueke, BMO ta ce magana ce ta rashin hankali da ba ta da tushe.
“An ja hankalinmu kan kalaman da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi ta bakin Daraktan yakin neman zaben ‘Bukola Saraki ’, Farfesa Iyorwuese Hagher a wani taron siyasa da aka yi a Kano inda ya yi wasu maganganu marasa tushe ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Watakila abin da ya fi daukar hankali daga wadannan zarge-zarge shi ne maganar da aka yi na cewa bangaren shari’a da na majalisa ba su da ‘yancin kai a karkashin wannan gwamnati.
“Muna kallon hakan a matsayin wani yunƙuri da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ya yi na murƙushe yabon da Majalisar Tarayya ta 9 kan yin abin da dace, wanda ‘yan Majalisar Tarayya da Saraki ya kasa yi a lokacinsu.
Ya kara da cewa: “Saraki ba shi ne shugaban majalisar dattawa na farko ba a fagen siyasar da muke ciki a yanzu, amma shi ne na farko tun 1999 da ya fara sukar hukumar zartaswa kai tsaye ta yadda matasan Najeriya suka dauka cewa ‘yan majalisar sun zama ‘yan amshin shata.
“Saboda haka ba abin mamaki ba ne a gare mu da ya yi hasarar babbar hasarar sa a fagen siyasa a abin da ya yi kama da zaben raba gardama kan ayyukansa na Shugaban Majalisar Dattawa.
BMO ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan da ’yan siyasar adawa da ke shirin yi wa gwamnatin Buhari sheda da duk wani nau’in ikrari da suke yi a yunkurinsu na ganin sun samu maki a siyasance.












































