Ƴan bindiga sun yi wa ƴan sanda kwanton ɓauna, tare da kashe guda biyar a Bauchi

bandits 1 750x430

Yan sanda guda biyar sun rasa rayukansu su a daren Asabar lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai hari unguwar Papa ta ƙaramar hukumar Darazo a jihar Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce wasu biyu sun samu raunuka a harin.

Wakili ya bayyana cewa jami’an ƴan sanda suna kan sintiri a Yankin Papa  lokacin da aka kai musu hari.

Ya ce an samu musayar wuta tsakanin jami’an ƴan sanda da masu kai harin, inda wasu daga cikin jami’an suka rasa rayukansu.

Cikin sunayen ƴan sandan da aka kashe a harin akwai Ahmad Muhammad, Mustapha Muhammad, Insp. Amarhel Yunusa, Insp. Idris Ahmed, da Corporal Isah Muazu.

Karanta: Mutane 38 cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar Kwara sun shaƙi iskar ƴanci

Wakili ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka sun hada da Insp. Isah Musa da Insp. Yusuf Gambo daga Sashen Bincike na Jihar.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi ya isa wurin harin domin yin bincike kai tsaye, sannan za a fitar da ƙarin bayani, ciki har da adadin wadanda suka rasa rayukansu.

Baya ga harin na Darazo, rundunar ta tabbatar da wani harin da aka kai a tsakiyar daren Asabar a ƙauyen Saya, Zalau a ƙaramar hukumar Toro, inda wani jami’in Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Alhaji Muhammadu Bakoshi, mai shekaru 55, ya rasa ransa, yayin da aka sace matarsa Hannatu Bakoshi mai shekaru 45, ‘yarsa Umaimah mai shekaru 13, da wani saurayi mai shekaru 20, Mubarak Dayyabu.

Kwamishinan ƴan sanda ya umarci Baturen yan sanda da kwamandan yankin Toro, tare da dukkan jami’an rassa, ƙungiyoyin tsaro, masu gadin gari, da mafarauta, su yi sintiri a daji domin kama masu laifi da ceto waɗanda aka sace.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here