Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga rushe gine-ginen dake kan titin jami’ar Bayero

imgonline com ua twotoone 00N8Es79jioScjoQ 750x430
imgonline com ua twotoone 00N8Es79jioScjoQ 750x430

Wata babbar kotun tarayya dake zamata a jihar Kano ta dakatar da gwamnatin Kano daga rushe gine-ginen dake kan titin jami’ar Bayero.

Jaridar Solacebase a baya rawaitu cewa gwamnatin Kano ta bayyana wasu gine-gine dake kan ganuwar Kano da zata rushe su, wadan da ta bayyana su a matsayin and gina su ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Hafsat Yahaya ta ba bada umarnin ne a ranar Talata, inda kuma kotun ta dage zaman ta zuwa ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 2023.

Wadan da suka shigar da karar sune Bashir Abdullahi Albasu da wasu mutane 19, inda wadanda ake karar sun hada da gwamnatin Kano, babban layan gwamnatin Kano da kuma hukumar tsara gine-gine ta jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here