Malamin nan Abduljabbar Nasir Kabara, ya nemi a dauke shari’ar da ake yi masa daga gaban babbar kotun shari’ar musulunci zuwa wata.
Malamin ya bukaci hakan a zaman shari’ar na ranar Alhamis, karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda ake tafiyar da shari’ar.
Tun da fari dai kotun ta umarci Lauyan Malam Abduljabbar Kabara da ya dawo ya ci gaba da bashi kariya.
A dai dai lokacin ne Kuma lauya mai gabatar da kara Barista Suraj Sa’ida (SAN) ya gabatar da lauyoyin dake taimaka masa, bayan haka ne kuma kotun ta duba bangaren Lauyan Malam Abduljabbar wato Barista Dalhatu Shehu amma baya ciki.
Kotun ta kuma waiwayi bangaren wanda ake kara tunda kotu bata ga Lauyansa ba, tare da tanbayarsa ko yana da masaniyar rashin zuwan Lauyan nasa, Amma Malamin ya bayyana cewa rashin zuwan nasa na da alaka da takardar da ya rubuta zuwa ga alkalin alkalai cewa a sauya masa kotu a mayar da shari’ar zuwa wata kotun.
A nan ne kuma kotu ta tambaye shi ko me yasa? Sai yace saboda yana so a sami alkalin da bashi da wata alaka da bangarorin shari’ar, sakamakon akwai abubuwa da dama da yake ganin babu adalci, inda ya yi zargin cewa wani lokacin ana canja masa bayanansa haka kuma ya sake zargin lauyoyisa na farko a kan sun yi yunkurin mayar da shi mahaukaci lokacin da aka tambayeshi a gaban kotu suka hanashi magana.
Shi kuma Lauyan gwamnati ya fadawa kotu cewa ba zasu yi Martani akan batun ba sakamakon Lauyan Malam Abduljabbar bai hallaci zaman kotun ba.
Daga karshe kotun tace ai ita ce ta nada Lauyan Malam Abduljabbar kuma bisa doka babu wani mutum ko Lauya da zai zo da wata dabara ta dakatar da sharia.
Don haka kotu ta umarci Lauyan Malam Abduljabbar wato Barista Dalhatu Shehu yazo yaci gaba da aikinsa idan kuma ba zai zo ba, Malam Abduljabbar zai iya sake Lauya kafin ranar dawowa kotun, inda ta dage zaman zuwa ranar 28 ga watan da muke ciki na Yuli domin sake gabatar da Malamin.