Sama da masu neman aiki 11,000 ne suka nemi guraban aikin yi, bayan da ake bukatar kasa da mutane 100 a hukumar Korafe-korafen Jama’a da yaki da cin Hanci da rashawa ta jihar Kano a rana ta uku da bude tashar neman aiki.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a Internet, ta ce an bude shafin neman aikin a ranar 7 ga Afrilu, 2025 kuma ana tsammanin rufewa da tsakar dare ranar Lahadi 13 ga Afrilun 2025.
Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya shaida wa SolaceBase ranar Alhamis cewa da karfe 6.30 na yamma, kimanin masu neman aiki 10,757 ne suka yi rajista a internet.
A cewarsa, zuwa karfe 10.00 na daren ranar Alhamis, sama da masu neman 11,000 ne suka gabatar da bukatar.
Rimingado, wanda ya danganta karuwar aikace-aikacen da yawan rashin aikin yi da kuma martabar da hukumar ta ke da shi a tsawon shekaru, duk kuwa da babbar bukatar da ake da ita na cewa masu nema dole ne su zama ‘yan asalin jihar.
Ya kuma yi nuni da cewa, wadanda da aka zaba kawai za a tuntube su, yana mai ba da tabbacin cewa ba za a tauyewa waɗanda suka cancanta hakkin su ba.
SolaceBase ta ba da rahoton cewa don cancanta, masu nema dole ne su mallaki ingantacciyar Lambar Shaida ta Ƙasa (NIN), Lambar sirri ta Banki (BVN), kuma dole ne su kasance tsakanin shekaru 25 zuwa 30.
Ana kuma sa ran masu nema su kasance masu lafiya a jiki, tunani, da hankali, kuma ba su da wata matsala.
Ana buƙatar matakin ilimi daga SSCE/NECO/GCE tare da credit biyar (ciki har da Lissafi da Ingilishi) zuwa OND, NCE, HND, da Digiri na farko a fannonin da suka dace.
Masu nema a matakin digiri dole ne su gabatar da takardar izinin NYSC ko takardar shaidar wuce shekarunsu.
Matsayin da ake neman ma’aikata a hukumar sun haɗa da:
– Mataimakin mai Bincike (GL 06) a matakin masu riƙe da OND da ND
– Mai bincike (GL 07) a matakin masu NCE da Difloma mai zurfi
– Sufeto II ga masu HND ko Digiri na Bachelor
Masu nema dole ne su sami ilimin kwamfuta na asali, musamman ƙwarewa a cikin Microsoft Office, yayin ake bukatar ƙwarewa a cikin sauran kayan aikin bayanai.