Kotun ta sake dakatar da ƴan sanda daga ci gaba da aiwatar da dokar hana kasim amfani da baƙin gilashin mota

tinted permit 716x430 (1)

Babbar kotun jihar Delta da ke zama a Orerokpe ta bayar da umarnin wucin gadi da ya hana rundunar ’yan sandan Najeriya kan hana aiwatarwa ko tilasta bin dokar lasisin baƙin gilashin mota da aka tsara za ta fara aiki a ranar biyu ga watan Janairun 2026.

Mai shari’a Joe Egwu ne ya bayar da umarnin a ranar Laraba yayin yanke hukunci a kan ƙarar da Isra’ila Joe ya shigar a gaban kotu yana ƙalubalantar sufeton janar na ’yan sandan Najeriya, rundunar ’yan sandan Najeriya da kuma kwamishinan ’yan sanda na jihar Delta.

A cikin ƙarar mai lamba HOR/FHR/M/31/2025, mai ƙarar ya nemi kotu ta hana ’yan sanda aiwatarwa, tilasta bin doka ko ɗaukar duk wani mataki na aiwatar da dokar hana izinin amfani da baƙin lasisin gilashin mota har sai an saurara kuma an yanke hukunci a kan ƙarar asali da ke gaban kotu.

Kotun ta kuma hana waɗanda ake ƙara tsayawa, tsoratarwa, kama, tsarewa ko karɓar kuɗi da ƙarfin tsiya daga mai ƙarar da sauran ’yan ƙasa ko masu ababen hawa da sunan aiwatar da dokar, tare da jaddada kare mutuncin ɗan Adam.

Karin karatu: NBA ta yi barazanar ɗaukar matakin raina kotu kan sufeton ƴan sanda da kakakin rundunar kan aiwatar da dokar baƙin gilashin mota

Mai shari’a Joe Egwu ya amince da duk buƙatun da mai ƙarar ya gabatar bayan yanke hukunci kan buƙatar gaggawa, tare da umarnin hana rundunar ’yan sanda da wakilanta aiwatarwa ko ci gaba da aiwatar da dokar hana lasisin amfani da baƙin gilashin mota har sai an yanke hukunci a kan ƙarar gaba ɗaya.

Kotun ta kuma hana amfani da asusun Parkway Projects, wanda aka bayyana a matsayin asusun mai zaman kansa, wajen gudanar da duk wata harkar gwamnati har sai an kammala sauraron ƙarar, tare da amincewa da hanyar isar da takardun kotu ta hannun kwamishinan ’yan sanda na jihar Delta da ke hedkwatar ’yan sanda a Asaba.

Duk da cewa mai ƙarar bai halarci zaman kotu ba, lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Kunle Edun SAN sun wakilce shi, kuma kotu ta sanya ranar ci gaba da sauraron ƙarar a ranar 24 gashirin watan Disamba, yayin da umarnin wucin gadin ya fara aiki daga ranar 17 ga watan Disamba, tare da tunatar da cewa wata babbar kotun tarayya da ke Warri a baya ma ta dakatar da aiwatar da wannan doka tare da umarnin a kiyaye matsayin da ake ciki har sai an kammala shari’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here