Akalla an ceto mutane tara a wani baraguzan gini da ya rufta a unguwar Lifecamp da ke babban birnin tarayya Abuja.
Ginin mai hawa biyar da ake ginawa ya ruguje ne da yammacin ranar Litinin.
Jami’an bada agaji ciki har da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, ya zuwa yanzu sun ceto mutane tara daga cikin wadanda suka makale a ginin da ya ruguje yayin da ake ci gaba da neman ceto.
A cewar hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, an garzaya da wadanda aka ceto zuwa asibiti.
Bayanan da aka tattaro na cewa otal din an ce na kamfanin Summit Villa hotel ne wanda ake ginawa bayan daukan tsawon lokaci.
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ginin ya ruguje ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin yayin da ma’aikatan ginin ke gudanar da aikinsu.
An dai bayyana cewa ginin wanda aka yi nisa da shi na masaukin otal, ya ruguje ne ba zato ba tsammani, ayayin da wani sashi ya makale ma’aikata da dama da ke ciki a lokacin da ginin ke rugujewa.