Zamu Dawo Da Tashar, PYRAMID FM, Cikin Hayyacin ta Ba da Jimawa Ba – Gwamnatin Kano

IMG 20230701 WA0022</a

A kokarin datake na sake farfado da tashar don cigaba da watsa shirye shirye bayan kwashe tsawon lokaci cikin mashasshara…

Gwamnatin Kano ta bayyana shirin ta na kulla alaka da gwamnatin tarayya domin sake dawo da cigaba da watsa shirye shirye dakuma magance katsewar shirye shiryen da tashar keyi.

Hon. Sulaiman Mukhtar, Dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar Madobi ya bayyana haka ayayin wata ziyarar bazata da yakai babbar tashar dake kan titin yako, a Madobi.

Sulaiman Mukhtar ya nanata kudirin gwamnatin jihar Kano na samar da kayan zamani dan inganta tashar a kokarin dawo da ita cikin hayyacin ta, la'akari da muhimmancin ta ga al'ummar kanawa.

"Ba kamar yadda nakeji ba, ya zama wajibi na godewa Manajan tashar bisa jajircewar sa a kokarin maido da tashar cigaba da watsa shirye shirye" Mukhtar.

Daganan Dan majalisar ya bada tabbacin cewa an kammala dukkan shirin da ya dace domin yiwa tashar garambawul ta hanyar maido da farin jinin tashar tareda shaharar ta wajan nisan zango a arewacin Najeriya.

Tun da farko dayake maida jawabi, Manajan tashar Kwamaret Abba Bashir ya godewa Dan majalisar a madadin gwamnatin Kano bisa kawo daukin gaggawa duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

"Wannan ziyara, ita ce irin ta ta farko a tarihi tun bayan zamowa ta Manaja, ba wani jami'in gwamnati da ya taba kawo mini makamanciyar irin wannan ziyara" Abba Bashir.

Kwamaret Abba Bashir yace akarkashin kulawar sa, zaiyi dukkan mai yiwuwa don ganin wannan mataki ya tabbata ba tareda tangarda ba.

Gidan rediyon na tarayya , an samar da shi aranar 19 ga watan Maris 2004, zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Kano Injiya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a kokarin sa na sadar da al'ummar karkara da ababen more rayuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here