Malami ya koka kan sumamen hukumar EFCC a ofisoshinsa da gidajensa

Abubakar Malami

Tsohon babban lauyan ƙasa kuma ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, ya bayyana damuwa kan samamen da jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC suka kai a wasu daga cikin ofisoshinsa da gidajensa da ke Abuja da jihar Kebbi, bayan wata sanarwa da ofishinsa ya fitar dangane da sashe na tara na rahoton kwamitin binciken shari’a na Ayo Salami.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello, ya sanya wa hannu, Malami ya bayyana cewa samamen sun faru ne jim kaɗan bayan fitar da sanarwar da ta shafi sashe na tara na rahoton Ayo Salami, wanda ke da alaƙa da shugaban hukumar EFCC na yanzu.

Sanarwar ta bayyana cewa jami’an EFCC sun gudanar da binciken ba tare da wani gargadi ko sanarwa ba, inda suka rika neman wasu takardu da ake zargin suna da alaƙa da sashe na tara na rahoton Ayo Salami.

Ofishin yaɗa labaran Malami ya bayyana wannan mataki a matsayin abin tayar da hankali sosai, yana mai cewa lokacin da aka gudanar da samamen na haifar da shakku kan yunƙurin tsoratarwa, ramuwar gayya da kuma barazana ga lafiyar ma’aikata da kuma Malami kansa.

Sanarwar ta kuma nuna cewa lamarin ya biyo bayan kiran da aka yi a bainar jama’a na neman shugaban EFCC ya janye hannunsa daga duk wani abu da ya shafi sashe na tara bisa zargin son zuciya, lamarin da ofishin Malami ya ce na iya barazana ga lafiyar mutum da kuma mutuncin doka.

Malami ya sanar da ’yan Najeriya da ƙasashen duniya cewa duk wani abu da ya same shi ko ma’aikatansa sakamakon wannan lamari za a ɗora alhakin ne kan irin wannan ɗabi’a, tare da kira ga ’yan jarida da al’umma su binciki dalilin da ya sa aka kai samamen nan take bayan ambaton sashe na tara, da hujjar doka da aka yi amfani da ita, da kuma dalilin amfani da ƙarfi da ɓoyewa maimakon bin doka.

Ofishin Malami ya kuma yi kira ga ƙungiyoyin farar hula, ƙwararru da masu kare haƙƙin ɗan Adam da su matsa wa gwamantin tarayya, ma’aikatar shari’a ta tarayya da ofishin babban lauyan ƙasa lamba domin fitar da cikakken rahoton kwamitin shari’a na Ayo Salami, musamman sashe na tara, domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da dawo da amincewar jama’a ga tsarin shari’a.

Malami ya kuma ce a shirye yake ya fuskanci duk wata sahihiyar hanya ta shari’a a gaban kotu mai hurumi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here