Tinubu ya tafi Turai gabanin taron da sa gudana a Abu Dhabi

Tinubu depart US 750x430 (1)

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bar birnin Legas zuwa nahiyar Turai a ranar Lahadi domin hutun ƙarshen shekara, tare da shirye-shiryen ziyara a hukumance zuwa birnin Abu Dhabi da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a Legas, inda ya bayyana cewa tafiyar na daga cikin jadawalin ayyukan shugaban ƙasa na ƙarshen shekara.

A cewar sanarwar, an tsara shugaban ƙasar zai halarci taron mako na dorewar raya kasa a Abu Dhabi na shekarar 2026, wani babban taro na duniya da ke haɗa shugabanni daga gwamnatoci, harkokin kasuwanci da ƙungiyoyin farar hula.

Ziyarar ta zo ne biyo bayan gayyata daga shugaban ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda ya gayyaci shugaban Najeriya domin halartar taron.

Taron makon dorewar raya kasa na Abu Dhabi na shekarar 2026 zai mayar da hankali kan haɗa buri da aiki a fannoni daban-daban kamar kirkire-kirkire, kuɗaɗe da bunƙasa jarin ɗan Adam, domin samar da hanyoyin ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa da haɗin gwiwar ƙasashen duniya.

Ana sa ran shugaban ƙasar zai dawo Najeriya bayan kammala taron.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here