Lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama kuma babban lauya na ƙasa, Femi Falana SAN, ya fayyace cewa kotun koli ba ta taɓa amincewa da rushe ko dakatar da tsarin Dimokiraɗiyya a kowace jiha ta tarayya a lokacin ayyana dokar ta baci ba, sabanin abin da wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna.
Falana ya bayyana hakan ne yayin wani sharhi kan hukuncin da kotun koli ta yanke a ƙarar da babban lauyan jihar Adamawa tare da wasu jihohi 19 suka shigar da gwamnatin tarayya, inda ya ce an yi kuskuren fahimtar hukuncin da kotun ta bayar.
Ya ce duk da cewa kotun ta yi watsi da ƙarar ne saboda masu shigar da ƙarar ba su da cancantar shigar da ita a gaban kotu, hakan bai hana kotun yin nazari kan muhimman batutuwan shari’ar ba, musamman waɗanda suka shafi ikon shugaban ƙasa a lokacin dokar ta ɓaci.
Falana ya jaddada cewa wasu sassan kafafen yaɗa labarai sun karkatar da ma’anar hukuncin, suna nuna kamar kotun koli ta amince da dakatarwa ko rushe rassan zartarwa da majalisa a matakin jiha a lokacin dokar ta baci, alhali wannan ba gaskiya ba ne.
Labari mai alaƙa: Kotun koli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta baci da dakatar da zaɓaɓɓun jami’ai
A cewar hukuncin jagora da Mai shari’a Mohammed Baba Idris ya gabatar, sashe na 305 na kundin tsarin mulkin 1999 bai bai wa shugaban ƙasa ikon rushewa ko dakatar da tsarin Dimokiraɗiyya a kowace jiha ba, ko da an ayyana dokar ta ɓaci.
Kotun ta kuma fayyace cewa kundin tsarin mulki ya raba ikon mulki tsakanin zartarwa, majalisa da shari’a, tare da rarraba su tsakanin matakan tarayya, jiha da ƙananan hukumomi, inda babu wani reshe ko mataki da ya fi wani iko a doka.
Kotun koli ta ƙara da cewa sabanin kundin tsarin mulkin wasu ƙasashe kamar Indiya da Pakistan, kundin tsarin mulkin Najeriya ya kauce wa bai wa shugaban ƙasa ikon kwace ko maye gurbin hukumomin jiha a lokacin dokar ta ɓaci ba, alamar jajircewar ƙasar wajen tsarin tarayya da ‘yancin ikon jihohi.
Falana ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da jama’a su rika bayyana hukuncin kotu daidai domin kauce wa rikitar da fahimtar doka da tsarin mulki.











































