Trump ya maka BBC a kotu, yana neman diyyar Dala Biliyan 10 kan yanke jawabinsa

trump and bbc 1

Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da ƙara a gaban kotu kan gidan talabijin na Birtaniya BBC, yana neman diyyar Dala Biliyan 10 saboda abin da ya kira ɓata suna da kuma gyaran jawabi da aka yi masa a wani shiri na talabijin.

Trump ya bayyana cewa BBC ta sauya tsarin wasu sassan jawabin da ya gabatar a ranar 6 ga Janairu, 2021, inda aka haɗa sassa daban-daban ta yadda aka nuna kamar yana ƙarfafa tashin hankali, alhali a cewarsa akwai sassan jawabin da ke kira ga zaman lafiya da bin doka.

Ƙarar ta bayyana cewa shirin da BBC ta fitar ya yaudari masu kallo, ya kuma jefa Trump cikin mummunan zargi a idon duniya, musamman ganin lokacin da aka fitar da shirin ya zo ne kusa da lokacin zaɓen shugaban ƙasa a Amurka.

Trump ya jaddada cewa wannan gyara da aka yi wa jawabin ya shafi mutuncinsa, siyasar sa da kuma harkokinsa na kasuwanci, inda ya ce an yi hakan ne da gangan domin cutar da shi a idon jama’a.

A nata ɓangaren, BBC ta riga ta amince cewa an samu kuskure a yadda aka shirya shirin, inda ta ce an yi rashin kyakkyawan hukunci wajen gyaran jawabin, duk da haka ta nuna cewa tana da kariya ta doka kan zargin ɓata suna.

BBC ya musanta ikirarin Trump na ɓata suna a ƙarƙashin doka, duk da cewa shugaban BBC Samir Shah ya aike wa Trump wasiƙar neman afuwa.

Rahoton ya kuma nuna cewa batun ya haifar da muhawara mai zafi kan ‘yancin kafafen yaɗa labarai da iyakar gyaran bayanai a cikin shirye-shiryen bincike, musamman idan ana magana kan fitattun mutane a duniya.

Masana doka sun bayyana cewa shari’ar na iya fuskantar ƙalubale, musamman saboda tsauraran ƙa’idojin shari’ar ɓata suna a Amurka, da kuma tambayar ko kotun Amurka na da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi kafar yaɗa labarai ta ƙasar waje.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here