Tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ta bayyana yadda marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fara kulle ɗakinsa bayan jita-jitar da ta bazu a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock cewa ita ce ta shirya kashe shi.
Ta kuma yi bayani cewa matsalar rashin lafiyar da ta tilastawa Buhari yin hutun jinya na tsawon kwanaki 154 a shekarar 2017.
Aisha Buhari ta musanta cewa, rashin lafiyar sa ba ta da wata alaƙa da asiri ko guba, illa dai ta samo asali daga tangardar tsarin abinci da kuma rashin kula da gina jiki yadda ya kamata.
Bayanan nata ya fito ne a cikin sabon littafin tarihin rayuwarsa mai shafuka 600 mai taken “Daga soja zuwa ɗan siyasa”: gadon Muhammadu Buhari, wanda Dakta Charles Omole ya wallafa kuma aka ƙaddamar da shi a fadar gwamnati.
Littafin mai babi 22 ya bibiyi rayuwarsa tun daga ƙuruciyarsa a Daura ta jihar Katsina har zuwa awanninsa na ƙarshe a asibiti a birnin London a tsakiyar watan Yuli na shekarar 2025.
A cikin littafin, Aisha Buhari ta nuna cewa ta dade tana kula da tsarin abinci da ƙarin sinadaran jiki na mijinta a lokuta na musamman, tsarin da ta ce ya taimaka wa mutum mai rauni da tarihin matsalolin rashin ingantaccen gina jiki ya ci gaba da samun ƙarfi.
Ta yi nuni da cewa tsofaffi na bukatar kulawa mai kyau da daidaito, tare da tabbatar da cewa babu wata cuta mai tsanani da ke damunsa idan an kiyaye tsarin.
Littafin ya bayyana cewa bayan sauya zama zuwa fadar Aso Rock, tsarin ya fara lalacewa.
Aisha Buhari ta kira taro da manyan ma’aikatan kusa da shugaban ƙasa, ciki har da likita, shugaban tsaro da mai kula da gida, domin bayyana tsarin ciyarwa da ƙarin sinadaran jiki da ta tsara.
Sai dai daga bisani jita-jita da tsoratarwa suka shiga tsakani, lamarin da ya sa shugaban ƙasa ya fara sauya wasu dabi’u, wajen jinkirin cin abinci kuma ya dakatar da shan abubuwan ƙarin sinadaran jiki.
Ta bayyana cewa tsawon kusan shekara guda, Buhari bai rika cin abincin rana ba, lamarin da ya kara tabarbarewar lafiyarsa.
Wannan ne ya kai ga yin tafiye-tafiyen jinya biyu zuwa ƙasar Birtaniya a shekarar 2017, inda ya mika ragamar mulki ga mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo.
Bayan dawowarsa, ya amince cewa bai taba yin rashin lafiya mai tsanani kamar wancan lokaci ba, har ma ya samu ƙarin jini.
Marubucin littafin ya bayyana cewa rashin kasancewar shugaban ƙasa ya haifar da jita-jita da hasashe iri-iri a cikin al’umma, amma Aisha Buhari ta karyata labaran shirin zuba masa guba.
Ta dage cewa asalin matsalar ita ce rushewar tsarin cin abinci da inganta gina jiki.
A birnin London, likitoci sun tsara masa ƙarin sinadaran jiki masu ƙarfi, inda a farko ya ji tsoro bai rika amfani da su yadda aka tsara ba, sai daga bisani ta sake karɓar kulawa har lafiyarsa ta farfaɗo cikin kankanin lokaci.
Littafin ya kuma tabo yanayin rashin amincewa da ya kewaye fadar shugaban ƙasa, inda Aisha Buhari ta yi zargin sa ido da na’urorin sauraro a ofishin shugaban ƙasa, tare da jaddada cewa tsoro da nauyin lamarin sun taka rawa wajen gajarta rayuwarsa.
Ta kuma karyata jita-jitar kama-da-wane da aka dade ana yadawa ta wani da ake kira Jibril na Sudan, tana mai cewa raunin sadarwar gwamnati ya ba da dama ga abubuwa na yau da kullum su rikide zuwa makarkashiya.













































