Dangote ya musanta zargin cewa Yana da hannu a kone zauren majalisar dokokin kogi.

dangote2
dangote2

Kamfanin Dangote ya musanta cewa yana da hannu kan tashin gobarar da ta kama a majalisar dokokin jihar Kogi kamar yadda gwamnatin jihar ta yi zargin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gobara ta kone ginin majalisar dokokin Kogi a safiyar ranar litinin.

Da yake zantawa da manema labarai yayin duba sasannin majalisar bayan kashe gobarar, Shugaban Majalisar ya ce yana zargin konewar majalisar wani zagon kasa ne zalla.
. Cikin wata sanarwa da jami’in kula da harkokin kasuwanci na rukunin kamfanonin Dangote Anthony Chiejina ya sanyawa hannu, ya musanta hannun su cikin tashin gobarar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ankarar da mu gameda wata sanarwar manema labarai da gwamnatin Kogi ta fitar, inda take zargin rukunan kamfanin Dangote da daukar nauyin tada gobara a majalisar dokoki da sanyin safiyar Litinin 10 gawatan Oktoba 2022.

Sanarwar ta ce Kwamishinan yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi Kingsley Fanwo ya zargi kamfaninmu da daukar nauyin kona majalisa.

Abaya dai Jaridar Solacebase ta bada labarin cewa gwamnatin Kogi da mahukuntan rukunin kamfanonin Dangote sun daura zare kan wanene hakikanin mamallakin kamfanin siminti na Obajana.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu jami’an gwamnatin Kogi suka yi yunkurin rufe kamfanin simintin, inda suka ce mallakin jihar ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here