Shugaban kungiyar malaman jami’o’i Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce nan ba da jimawa ba kungiyar za ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni takwas tana yi.
Farfesa Osodeke ya bayyana haka ne a wani taro dasuka gudanar da shugabannin majalisar wakilai a Abuja.
Ya ce daga abin da kungiyar ta gani a wurin taron “akwai alamun haske a karshen tattaunawar.
Ya kuma yi fatan cewa shiga tsakani da shugabannin majalisar yayi shi ne na karshe saboda dalibai, inda ya kara da cewa fafutukar da ASUU ta yi ne neman inganta tsarin ilimi da jami’o’i na kasar nan.
“Muna fatan nan da ‘yan kwanaki za mu kawo karshen wannan yajin aikin da mukeyi.
Ya ce ya kamata daliban kasashen ketare su rika biyan jami’o’in Najeriya kudi mai kauri, yayin da ya nuna damuwa kan yadda wasu nagartattun malamai suka bar aikin zuwa kasashen waje.
Ya cigaba da cewa, “Muna godiya bisa shiga tsakani da shugaban majalisar wakilai yayi kuma dole ne mu hada kai domin kowane dan Najeriya ya yi alfahari da jami’o’in da muke da su.”
Femi daganan ya ce shugabannin majalisar sun tabbatar da cewa an samar da dukkan bukatun ASUU da sauran su a kasafin kudin 2023.
Ya ce an saka Naira milyan dubu 470 a cikin kasafin kudin 2023 don biyan bukatun kungiyar ASUU.
“An warware matsalar UTAS kamar yadda gwamnati da ita kanta ASUU suka amince kuma dukkansu za su zauna su amince da sanya hannu a tsarin biyan kudin IPPIS.