WAEC ta fara gwajin rubuta jarrabawar ta hanyar kwamfuta

WAEC WAEC 691x430

Hukumar shirya jarrabawar yammacin Afirka ta Yamma (WAEC) ta gudanar da gwajin rubuta jarrabawar essay ta hanyar kwamfuta, a shirye-shiryen kaddamar da jarrabawar WASSCE ta kwamfuta ga daliban makarantu a shekarar 2026.

Wannan gwaji ya gudana ne a cibiyar horaswa da gwaji ta WAEC da ke Ogba, Legas, karkashin jagorancin shugaban ofishin WAEC na kasa, Dakta Amos Dangut.

Daliban sakandare na babban aji ne suka halarci gwajin wanda aka tsara domin su saba da tsarin jarrabawar kwamfuta da ke hada tambayoyin zabi daya daga rubutattun essay.

Dangut ya bayyana cewa wannan shiri yana da nufin shirya dalibai domin shiga jarrabawar kwamfuta gaba daya tare da rage gibi na fasaha tsakanin makarantu a sassan kasar.

Ya ce wasu makarantu za su yi dukkan bangarorin jarrabawar ta hanyar kwamfuta, yayin da wadanda ke yankunan da ba su da isassun na’urori za su ci gaba da rubuta ta da hannu.

Dangut ya kara da cewa tsarin zai inganta daidaito da saukin gudanar da jarrabawa ga kowane dalibi, tare da tabbatar da sahihanci da amincin tsarin WAEC.

Ya kuma shawarci dalibai su rungumi karatu da fasahar zamani, yana mai cewa jarrabawar kwamfuta ita ce makomar ilimi a duniya.

 

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here