Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, Atiku Abubakar, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, a ranar Asabar sun hallara a Jihar Kano domin daurin auren ‘yar tsohon Gwamnan Jihar, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.
Rahoton SolaceBase ya bayyana cewa mahaifan ango da amarya, Dahiru Mangal da Rabiu Kwankwaso, tare da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da mataimakinsa, Aminu Abdusalam Gwarzo, duk sun halarci bikin.
Daurin auren ya gudana ne a fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.