Wani babban koma-baya na siyasa ya dabaibaye jam’iyyar APC a jihar Kano, yayin da Mustapha Hamza Buhari Bakwana, babban makusancin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya koma jam’iyyar NNPP a hukumance.
SolaceBase ta ruwaito cewa Bakwana ya kuma yi watsi da naɗa shi a matsayin babban mai taimaka wa mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibril.
Da yake jawabi ga magoya bayansa a Kano yau Laraba, Bakwana ya ce, shugabannin APC sun yi watsi da su kuma sun ci amanar su, Bakwana wanda ya taɓa zama mashawarci na musamman kan harkokin siyasa ga Ganduje a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kano, ana yi masa kallon ɗaya daga cikin manyan masana siyasar da ke tare da Ganduje a yankin Arewa maso Yamma.
Ana dai kallon ficewar tasa a matsayin babban koma-baya ga yunƙurin gangamin jam’iyyar APC a Kano, jihar da ta kasance fagen fama a zaɓen shekerar 2027 da ke tafe.
Matakin nasa ya kuma nuna rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar APC, musamman a Kano, inda a watannin baya-bayan nan rikici ya kaure tsakanin ɓangarorin da ke biyayya ga Ganduje da masu goyon bayan shugabancin jihar.













































