Gwamnatin kasar Mali ta nemi yan kasar ta dasu bata hadin kai wajan goyon bayan wukunci da ta yanke na ficewa daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Afirka ta Yamma (ECOWAS).
A cikin wata wasika da manene ma labaran kasar suka gane wacce ta fito daga ofishin ministan harkokin matasa da wassani na kasar, ta nuna yadda gwamnatin kasar take neman goyon bayan matasan kasar bisa wukuncin data yanke na ficewa daga Kungiyar ECOWAS.
Wasikar ta ce “Gwamnatin Mali, ta hannun Ministan Matasa da Wasanni, na kira ga jama’a da su hada kai don goyon bayan hukuncin da gwamnatin Mali, Burkina Faso da kuma Nijar na ficewa daga kungiyar ECOWAS.”
Idan dai za’a iya tunawa, kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar sun sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS, bayan shafe tsawon lokaci ana taƙaddama a tsakanin kasashen da kuma kungiyar ECOWAS.
Sai dai Kungiyar ta ECOWAS ta bayyana rashin jin dadin ta bisa wukunci da kasahen suka yanke na ficewa daga kungiyar.