Shugabannin kamfanin matatar man fetur na Dangote sun ce matatar na ci gaba da aiki yadda ya kamata bayan wata gobara da ta kama a yau Laraba.
A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar, wadda ta wallafa a shafinta na X, wacce ta samu sa hannun mai magana da yawun matatar, Anthony Chiejina ta ce “Mun samu nasarar kashe wata ƴar gobara da ta tashi a kamfaninmu a yau Laraba 26 ga watan Yuni.
Karin labari: “Majalisar dattijai ba ta amince a sayi sabbin jirage ga shugaba Tinubu ba” – Akpabio
“Babu wata damuwa domin matatar man fetur ɗin na ci gaba da tafiyar da lamuranta sannan kuma babu wanda ya samu rauni” in ji sanarwar.