Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar ba ta amince da a sayi sabbin jiragen shugaban ƙasar da na mataimakinsa ba.
Akpabio ya yi watsi da wani rahoto da ke nuna cewa majalisar dattawan za ta amince da sayen sabbin jiragen sama ga Bola Tinubu da Kashim Shettima duk da ƙalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shi.
Wannan rahoto ya biyo bayan shawarar da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro ya bayar na sayen sabbin jiragen sama saboda matsalolin da jiragen shugaban ƙasar ke fuskanta.
Karin labari: Daliban sakandire 6 sun nutse a kogi bayan dawowa daga jarrabawa a Kaduna
A kwanakin baya ne shugaba Tinubu ya yi amfani da jirgin sama na ƴan kasuwa domin halartar bikin rantsar da shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afrika ta Kudu.
Fadar shugaban ƙasar ta kare buƙatar samar da sabbin jiragen sama ga shugaban da mataimakinsa yayin da take mayar da martani ga sukar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi ya yi, wanda ya kira shirin da rashin hankali.
Karin labari: Kotu ta umarci a ƙwace dala miliyan 1.4 daga hannun Emefiele
A wata sanarwa da mai taimakawa Akpabio kan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom ya fitar, ya musanta cewa majalisar dattawa ta amince ƙudirin samar da sabbin jiragen sama yayin da yake magana a Maiduguri, jihar Borno, bayan ziyarar jaje da ya kai wa Sanata Tahir Monguno.
Ya danganta rahoton na karya ga masu yaɗa farfaganda kuma ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi addu’ar samun nasara ga gwamnati.