Ƴan mata 15 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Sokoto

1683666765694
1683666765694

Akalla ƴan mata 15 ne suka rasu bayan kifewar kwale-kwale a ƙauyen Dandeji da ke karamar hukumar Shagari na jihar Sokoto.

An ruwaito cewa ƴan matan na kan hanyarsu ta zuwa wani daji da ke kusa domin neman itace lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a safiyar yau Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan mata sama da 40 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da lamarin ya faru, a cewar shaidu.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce an gano gawawwaki 15 kawo yanzu, inda ya ce masu ninƙaya na ci gaba da neman sauran waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Shugaban karamar hukumar ta Shagari, Aliyu Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana shirin yi wa mutanen jana’iza.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here