Hukumar dake kula da kwashe gobara ta kasa ta biya sama da jami’anta 2000 hakkunan su, wanda da suka hada dana karin girma da kuma albashin su da ya makale.
Mai magana da yawun hukumar na kasa, Abraham Paul, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya ce biyan ma’aikatan na daya daga cikin alkawarin da sabon shugaban hukumar na kasa, Mista Jaji AbudulGaniyu, ya yi na bunkasa walawalar jami’an hukumar.
Sanarwar tace biyan kudin ya fara ne tun daga shekarar 2016 har zuwa wanan watan da muke ciki.
“A lokacin da yake bikin murnar cikar sa kwanaki dari da kama aiki, shugaban namu ya yi alakawarin biyan duk wani hakkunan ma’aikatan da aka rike musu ba’a biya su a baya ba, sanan kuma ya yi alakawarin ingantawa tare da habbaka walwalar jami’an hukumar.”
“Yanzu haka ya fara cika alkwarin da ya dauka ne, kuma zai yi kokarin sa don ganin an biya kowa hakkin sa.” Inji Sanarwar.












































