Garuruwa uku da aka fi sace mutane a kan titin Kaduna-Abuja

121759959  102654040 mediaitem102654039.jpg
121759959 102654040 mediaitem102654039.jpg

Matsalar garkuwa da mutane na ci gaba da tayar da hankulan jama’a a arewacin Najeriya. Lamarin ya fi ta’azzara a jihohin arewa maso yamma irin su Zamfara da Katsina da Kaduna.

Sai dai hankulan jama’a na ƙara karkata kan titin Kaduna zuwa Abuja sakamakon sace mutanen da har yanzu ba a san adadinsu ba da kuma kashe wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

A baya ana ta murna cewa an samu saukin matsalar garkuwa da mutane a wannan shahararriyar hanya.

Hukumomin Najeriya sun ɗauki matakan kariya tare masu yawa da suka hada da girke sojoji masu yawa ciki har da wasu sojoji mata da suke sintiri a kan titin.

Masana harkokin tsaron sun ce wadannan matakai sun yi matukar tasiri a zahiri, amma kuma abin da ya faru a karshe makon jiya ƙara tayar da hankulan al’ummar kasar.

Bayanai sun nuna cewa akwai garuruwa uku da masu garkuwa da mutane suka fi cin karensu babu babbaka a wannan yanki – garuruwan su ne Jere da Katari da kuma Rijana.

Katari

Garin Katari yana da nisan kilomita 61 daga Kaduna kuma yana daya daga cikin garuruwa masu matukar haɗari da masu garkuwa da mutane ke sace mutane.

Jere

Garin Jere mai nisan kilomita 105 na yankin karamar hukumar Kagarko a Kudancin Kaduna, kamar dai Katari yake a wajen haɗari.

Mafi yawan hare-haren da ake kai wa Katari suna da alaƙa da Jere saboda suna kusa da juna.

Rijana

Rijna shi ne gari na uku mai hadari wanda ke da nisan kilo mita 59.4 daga Kaduna. Wuri ne da aka girke sojoji da ‘yan sanda amma hakan bai hana masu garkuwa da mutane gudanar da ayyukansu ba.

Gari ne da ake yi masa hangen dala ba shiga birni ba, domin da yawa suna zuwa Rijana za su ji kamar sun shiga Kaduna daga Abuja, amma idan daga Kaduna ne zuwa Abuja to ana kallonsa a mafarin tafiya.

(BBC)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here