Hukumar kula da Abuja ta rufe Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya

Abuja seal 678x381 1
Abuja seal 678x381 1

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, ta rufe ma’aikatar ayyuka ta tarayya da hukumar tabbatar da daidaito a ayyuka ta tarayya da kuma Merit House dake Maitama kan bashin naira biliyan 10 da hukumar kare muhalli ta Abuja ke bin su.

Da yake yiwa manema labarai karin haske yayin atisayen, Daraktan hukumar kare muhallin Mista Osilama Briamah, ya ce hukumar ta gudanar da ayyukan sharar gida da sauran ayyukan kula da muhalli ga ma’aikatun kuma sun ki biya.

Ya bayyana cewa hukumar tana bin basukan makudan kudade ba tare kuma da sun yi musu bayani ba.

“Mun yi iya bakin kokarinmu domin mu dai-daita dasu yadda zasu iya biyan mu basukan da muke bin su, amma hakan bai samu ba”.

“Wannan yasa muka garzaya KOTU inda aka bamu damar garkame ma’aikatunsu “.

“Atisayen da yanzu ne muka fara Muna fatan zamu cimma dukkan Ofisoshin Gwamnati dana masu zaman kansu, wadanda muke bin su bashi”. Inji shi.

A baya dai babbar kotun Majestari dake zaune a Wuse Zone 2 Abuja ta aike da sammace ga Ma’aikatun da ake bi basukan, kan su gurfana a gabanta ranar 30 ga watan Maris, amma suka gaza martaba umarnin kotun.

Jadawalin basukan dai ya nuna cewa ana bin Ma’aikatar ilimi Naira Miliyan 25 da dubu 838 da 275, sai Ma’aikatar tsaro da ake binta Naira Miliyan 17 da dubu 220 da 775, yayin da Hukumar tabbatar da daidaito a ayyuka ake binta Naira Miliyan 10 da dubu 128 da 906 da kobo 25.

Sauran sune Hukumar kula da Ma’aikata da bashinta ya kai Naira miliyan 2, da dubu 451,da 649 da kobo 50, Hukumar tattara kudaden haraji ta Revenue Mobilisation and Fiscal Commission, da aka biyo ta Naira Miliyan 21 da dubu 683 da 750 da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ake binta Naira Miliyan 14 da dubu 204 da 843 da kobo 75.

Kazalika Ma’aikatar kula da masana’antu da zuba hannayen jari an biyo ta bashin, Naira miliyan 19 da dubu 222 da 287 da kobo 50, Yayin da aka biyo Ma’aikatar ayyuka ta Tarayya Naira Miliyan 9 da dubu 998 da 625, itama dai Hukumar kare rayuka da dukiyoyin al’umma ta Civil Defense dake Wuse a Abuja, an biyo ta tsabar kudi har Naira Miliyan 16 da dubu 583 da 031 da kobo 25.

Dayake jawabi babban mai taimakawa Ministan birnin tarayya Abuja na musamman kan dubawa tare da tabbatar da an bi doka Mista Ikharo Attah, yace atisayen ya biyo bayan umarnin Ministan Birnin tarayya Abuja da kuma babban sakataren hukumar lura da Birnin Tarayya na cewa aje a tattaro bashin da ake bi.

Attah ya kara da cewa hukumar kula da Birnin Tarayya ta damu matuka bisa gaza biyan basukan da ake bin wasu ma’aikatu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here