Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado kujerarsa ta shugabancin Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi ta cin hanci ta jihar.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce gwamnan ya mayar da shi ne nan take bisa biyayya ga umarnin kotu.
Tsohuwar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Muhuyi Magaji daga kujerarsa.
Sai dai ya garzaya kotu bisa da’awar cewa an dakatar da shi ba bisa ƙa’ida ba.
Cikin watan Yunin nan ne kuma kotun ta tabbatar da shi akan kujerarsa.