Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta bukaci da a cafke babban daraktan hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, bisa abinda matarsa Aisha Yusuf Bichi ta aikata na cin zarafin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.
Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar na ƙasa, Uche Nnadi, ranar Litinin a Abuja, ta bayyana cewa, cigaba da zamansa a matsayin shugaban DSS, babbar barazana ce.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Nnadi yace irin wadannan abubuwan ba wadanda za’a kyale bane, domin abubuwa ne da suke nuni da cewa za’a karya alkawarin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dauka, na tabbacin gudanar da zaɓen shekarar 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.













































