Tsohon gwamnan jihar Benuwai da ya sauka ranar 29 ga watan Mayu, Samuel Ortom, yanzu haka yana tsare a hannun hukumar yaƙi da rashawa EFCC.
Wakilin jaridar Daily Trust ya tattaro cewa hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa, ta gayyaci tsohon gwamnan ne domin amsa wasu tambayoyi.
Mista Ortom ya shiga harabar ofishin EFCC da ke layin Alor Gardon a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai a motarsa da misalin ƙarfe 10:08 na safiyar ranar Talata, 20 ga watan Yuni.