Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Jarumi Sahir Abdul, na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wanda akafi sani da Malam Ali na shirin Kwana Casa’in ya bayyana ficewarsa daga masana’antar.
Sahir ya bayyana ficewar ne a ranar Alhamis 30-05-2024 jim kada bayan Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya jaddada cewa ba za su yi wa jarumin afuwa ba.
Karin labari: Daliban jihohin Najeriya za su amfana da tsarin bada lamunin gwamnatin tarayya – Jami’i
Jarumin ya nemi afuwar duk wadanda ya bata wa rai a baya kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.
Idan dai ba’a manta ba a shekarar 2023 ne Hukumar Tace Fina-finai ta Kano ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali na Kwana Casa’in daga Fina-finan Hausa har na tsahon shekaru biyu.
Karin labari: ‘Yan Najeriya sun soki kudirin maido da tsohon taken kasa
Hukumar tace hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka yi a kansa na cewa yana yada bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.
Hukumar ta ce ta gayyace shi amma ya bijirewa amsa gayyatar ta.