Kotun babbar birnin tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Chizoba Orji, ta yi watsi da ƙarar batanci da gwamnatin tarayya ta shigar kan Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kotun ta ɗauki wannan mataki ne bayan lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara ya nemi a janye shari’ar gaba ɗaya, lamarin da ya sa lauyan Sanata Natasha ya roƙi kotu ta yanke hukuncin watsi da shari’ar bisa wannan buƙata.
Kotun ta amince da roƙon, inda ta watsar da shari’ar tare da sallamar masu bada beli da kuma umartar a mayar musu da dukkan takardun da aka karɓa a lokacin shari’ar.
Mai shari’a Chizoba Orji ta bayyana cewa wannan ci gaban ya nuna muhimmancin takatsantsan wajen amfani da ikon gurfanarwa, tare da buƙatar mutunta doka da tsarin dimokuraɗiyya domin tabbatar da zaman lafiya da adalci.
Bayan fitowa daga kotu, Sanata Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa hukuncin ya tabbatar da matsayarta, inda ta nuna aniyarta ta ci gaba da wakiltar al’ummarta tare da kare haƙƙin dimokuraɗiyya na ‘yan ƙasa.
Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar ne bisa zargin kalaman batanci da Sanatar ta yi a wani shirin talabijin kai tsaye, inda aka danganta kalaman da zargin cutar da martabar Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, amma kotu ta kawo ƙarshen shari’ar bayan janyewar gwamnati.













































