Iyalan Sojojin da suka rasu sun koka kan watsi da su a bikin tunawa da ƴan mazan jiya

IMG 20260115 102916 768x578 1 750x430

Zawarawan jaruman sojojin Najeriya da suka rasu sun bayyana halin ƙunci da watsi da suke fuskanta, musamman a daidai lokacin da tsadar rayuwa ke ƙaruwa da kuma matsin tattalin arziki ke tsananta.

Wadannan zawarawa sun bayyana hakan ne yayin bikin tunawa da sojoji na Najeriya da aka gudanar a dandalin Tafawa Balewa da ke tsibirin Victoria a jihar Legas, inda suka halarci taron domin girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ana gudanar da bikin tunawa da sojojin Najeriya duk shekara domin tunawa da girmama gudummawar sojojin da suka gabata da na yanzu wajen kare ƙasa.

Hajiya Helen Amodu, mai kula da kungiyar zawarawan sojoji ta Navy Town, ta bayyana cewa tun shekaru goma bayan rasuwar mijinta, har yanzu ba a biya ta inshorar rayuwar da ya bari ba, lamarin da ke kara mata nauyi wajen kula da ‘ya’yanta.

Ta bayyana cewa bayan rasuwar miji, zawarawa kan bar barikin sojoji su koma rayuwar farar hula, inda suke fuskantar matsaloli masu yawa, wanda hakan ya sa suka kafa kungiya domin tallafa wa juna, duk da cewa tallafin da gwamnati ke bayarwa ba ya zuwa a kan lokaci.

Haka zalika, Hajiya Yemi Enoch, wadda ta shafe shekaru bakwai a matsayin bazawara, ta jaddada cewa duk da farin cikin tunawa da jaruman da suka rasu, akwai bukatar a kara daukar matakai masu karfi domin kula da iyalan sojojin da suka mutu yayin aiki, musamman yara masu karatu da iyalai masu bukatu.

A bangarensa, Shugaban kungiyar tsoffin sojoji ta Najeriya a jihar Legas, Akeem Wolimoh, ya bayyana cewa kowace shekara ana rarraba tallafi ga tsoffin sojoji da zawarawansu, inda gwamnatin jihar Legas ta bayar da buhunan shinkafa 500 da sauran kayan abinci da za a rarraba, tare da shirin tallafa wa yaran zawarawa ta hanyar shirye-shiryen ilimi, domin girmama jaruman da suka sadaukar da rayukansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here