Zan bai wa Super Eagles alƙawarin Dala 500,000 duk da rashin nasara a gasar AFCON a wasan kusa da na karshe-Abdul Samad Rabiu

Super Eagles sabo 750x430

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yaba wa tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles kan kwazo da jajircewar da suka nuna a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.

Ya tabbatar da cewa alkawarin kudin da ya yi na bai wa tawagar la’ada har yanzu yana nan, duk da faduwarsu a wasan daf da karshe da suka yi da mai masaukin baki kasar Morocco.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta sha kaye mai radadi a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 bayan da ta sha kashi da ci 4–2 a bugun fenariti daga kasar Morocco, bayan wasan ya kare babu ci babu na kusa har bayan karin lokaci a filin wasa na Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.

Abdul Samad Rabiu ya bayyana cewa jarumta, hadin kai da jajircewar ‘yan wasan sun cancanci alfahari da murnar kasa baki daya, inda ya nuna cewa kokarinsu ya faranta ran ‘yan Najeriya a gida da kasashen waje.

Labari mai alaƙa: Morocco ta doke Najeriya, inda ta samu tikitin wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka

Ya ce, sakamakon wasa ba lallai ya nuna irin kokarin da aka yi ba, amma yunkurin fafutuka da hadin kan da tawagar ta nuna sun yi tasiri sosai ga al’umma, tare da tabbatar da cewa za a biya su kudin dala 500,000 a matsayin girmamawa ga aikinsu da farin cikin da suka bai wa kasa.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Abdul Samad Rabiu ya yi wannan alkawari tun bayan nasarar da Najeriya ta samu da ci 2–0 a kan kasar Algeria a wasan daf da kusa da na karshe.

Ya kuma karfafa gwiwar ‘yan wasan da su ci gaba da dagewa domin darussan da aka koya daga gasar su zama ginshikin nasarori a gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here