Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa reshen jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 20 bisa yunkurin shigar da miyagun kwayoyi nau’in tabar wiwi ta Indiya cikin gidan gyaran hali da ke harabar babbar kotun Kano.
Bayanin ya nuna cewa jami’an hukumar sun kama matashin ne yayin da suke rakiyar fursunoni zuwa kotu domin sauraron shari’o’insu daban-daban.
Anan ne aka gano matashin, wanda ke zaune a unguwar Tishama Hotoro a Kano, dauke da tabar wiwi ta Indiya da aka boye cikin burodi.
Jami’an gidan gyaran hali na Goron Dutse ne suka gano kayan yayin binciken tsaro da aka saba yi kafin shiga kotu, inda aka tabbatar da cewa an nannade tabar wiwin cikin burodi domin mikawa wani fursuna a lokacin zaman kotu.
Rahoton ya kara da cewa babban jami’in kula da gidajen gyaran hali na jihar Kano, Ado Inuwa, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa domin ci gaba da bincike da daukar matakin shari’a.
Labari mai alaƙa: Kano: Hukumar kula da gidajen yari ta kama mutane biyu kan yunƙurin shigar da miyagun ƙwayoyi ga fursunoni a kotu
Ado Inuwa ya yaba wa jami’in da ke kula da gidan gyaran hali na Goron Dutse, ACC Kafilu Abdullahi, tare da sauran jami’an da suka nuna kwarewa, jajircewa da kula wajen hana shigar da haramtattun abubuwa cikin gidajen gyaran hali.
Ya sake jaddada kudurin hukumar gyaran hali ta kasa na tabbatar da tsaro da tsaftar gidajen gyaran hali daga miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano, tare da bukatar iyaye da masu kula da yara su ja kunnen ‘ya’yansu daga shiga harkokin aikata laifuka.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa hukumar ta dakile makamancin wannan yunkuri a baya-bayan nan, a wani bangare na ci gaba da kokarin rage aikata laifuka da shigar da miyagun kwayoyi cikin gidajen gyaran hali.












































