Kotun Koli Ta Dakatar Da Dokar Hana Amfani Da Tsaffin Naira 

BREAKING 1 1
BREAKING 1 1

A yau Laraba, kotun kolin Najeriya ta dakatad da yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na hana amfani da tsaffin takardun Naira daga ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Kwamitin Alkalan kotun guda bakwai karkashin jagoranicin Justice John Okoro, ya dakatad da shirin bisa karar da wasu gwamnonin Arewa uku suka shigar kotun. Gwamnonin sun hada da Nasir El-Rufa’i na Kaduna, Muhammad Bello Matawalle na Zamfara, da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Gwamnonin uku sun bukaci kotun ta dakatad da shirin hana amfani da tsaffin takardun Naira da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here