Za A Kara Mafi Karancin Albashin Ma’aikata A 2024

WhatsApp Image 2022 06 22 at 5.26.30 PM
WhatsApp Image 2022 06 22 at 5.26.30 PM

Ministan Kwadago da Ayyuka Chris Ngige ya ce shirye-shirye sun yi nisa don kara mafi karancin albashi a shekarar 2024.

Ngige ya kuma gargadi kungiyoyin kwadago da su daina tsoma kansu a harkokin gwamnati da kuma nada mukamai.

Ya kuma ce ‘ya‘yan kungiyar na karya dokar da ta tilasta wa duk wani sabon dan kungiya samun horo na musamman a makarantar horon kwadago ta (MINILS).

Kazalika jaridar Aminiya ta rawaitu a taron Kungiyar Kwadago na Kasa karo na 13 da aka gudanar ranar Talata a Abuja, ya ja hankalin ‘yan kwadagon da su tabbatar da gwamntocin jihohi na aiwatar da Dokar Diyyar Ma’aikata ta 2010 (ECA) da doka ta ce a biya su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here