PDP: Muhuyi Magaji ya canja aniyarsa ta takarar gwamna zuwa sanata

Muhuyi Magaji Rimin Gado
Muhuyi Magaji Rimin Gado

Mai neman takarar gwamnan Kano a jam’iyar PDP Barista Muhuyi Magaji Ramini-Gado zai tsaya takarar sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, biyo bayan janye ra’ayin sa da ya yi na takarar gwamna.

Rimingado wanda shi ne tsohon shugaban hukumar kar6ar kurafi da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ya ce, ya fasa tsayawa takarar gwamnan ne  biyo bayan  rarrashinsa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi, akan ya hakura da takarar gwamna, ya yi ta sanata.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, jam’iyar ta PDP ta gudanar da za6en cikin gida na gwamnoni a kasa baki daya.

sai wani tsagi na jam’iyyar a kano su ma  sun yi nasu za6en inda tsagin Shehu Wada Sagagi wanda kutu ta ayyana shi a matsayin shugaban jam’iyyar, suka yi za6ensu a shalkwatar jam’iyyar, inda kuma daya tsagin na su mataimakin shugaban jam’iyyar Bello Hayatu gwarzo suka yi nasu za6en a cibiyar horar da matasa sana’o’i ta Sani Abacha.

Mai taimakawa Muhuyi Ramin-Gado, Nafiu Danlami ya tabbatar wa Jaridar Solacebase cewa, Rimin-Gado ya karbi fom din takarar sanatan Kano ta Arewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here