Hukumar Zabe Mai Zaman kanta ta kasa ta rantsar da sabbin kwamishinonin zabe 19 da aka nada gabanin manyan zabukan shekarar 2023.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya rantsar da kwamishinonin a hedikwatar hukumar da ke abuja, ya ja kunnen jami’an da ka da su kasance masu ziyartar gidajen gwamnati domin hakan zai saka su cikin tsaka mai wuya.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuli ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen mutane 19 da aka nada a matsayin kwamishinonin hukumar zaben ga majalisar dattawa domin tantancewa.
14 daga cikin kwamishinonin zaben sabbi ne, aka sake karin wa’adi na biyu ga mutane 5.
Cikin wadanda aka sabinta kujerun su sun hada da Ibrahim Abdullahi Adamawa Obo Effanga Cross River Umar Ibrahim Taraba Agboke Olaleke Ogun da Farfesa Samuel Egwu Kogi.
Sauran sune Onyeka Ugochi Imo Muhammad Bashir Sokoto Ayobami Salami, farfesa, Oyo Zango Abdu Katsina Sarauniya Agwu Ebonyi da Agundu Tersoo Benue Yomere Oritsemlebi Delta Yahaya Ibrahim, farfesa, Kaduna; Nura Ali Kano; Agu Uchenna Enugu; Ahmed Garki FCT; Hudu Yunusa Bauchi; Uzochukwu Chijioke, farfesa, Anambra da Mohammed Nura Yobe.
Shugaban hukumar ya lura cewa hukumar ta yi namijin kokari wajen gyara tsarin zabe tare da bullo da sabbin abubuwa wadanda aka amince da ingancin su a harkokin zaben.
Farfesa Yakubu ya jaddada cewa, ya zama wajibi kwamishinonin zaben ba za su yi aiki a cikin jihohin su na asali ba a duk lokacin aikin su.
Cikin sabbin kwamishinonin aka tura sun hada da: Farfesa Uzochukwu Chijioke da aka tura zuwa Abia, Barr. Nuhu Yunusa Adamawa, Sarauniya Elizabeth Agu Anambra, Mohammed Bulama Nura Bauchi, Farfesa Samuel G. Egwu (Benue, Yomere Gabriel Oritsemolebi Cross River, Onyeka Pauline Ugochi Ebonyi Obo Effanga Edo, Farfesa Ayobami Salami Ekiti, Umar Ibrahim Gombe, Farfesa Sylvia Uchenna Agu (Imo), Farfesa Muhammad L. Bashar Jigawa, Amb. Abdu Abdussamad Zango (Kano) Farfesa Yahaya Makarfi Ibrahim Katsina Ahmed Yushau Garki Niger, Dr. Agboke Mutiu Olaleke Osun Dr. Agundu Oliver Tersoo Plateau Dr. Nura Ali Sokoto Ibrahim Abdullahi Yobe.
Hakanan kwamishinonin huɗun da aka sabunta wa’adinsu su ne: Dr Adediran Rahmon wanda aka sake tura shi daga Ekiti zuwa Oyo. An mayar da Mahmuda Isah daga Jigawa zuwa Kaduna.
Yayin da aka mayar da Johnson Alalibo zuwa Rivers, Kuma aka tura Chukwuemeka J. Chukwu zuwa Enugu.













































