
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhinin rasuwar Dakta Cairo Ojougboh tsohon Darakta na Hukumar Raya Neja Delta NDDC.
Wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Alhamis, ya ce Ojougboh ya rasu ne a ranar Laraba.
Ngelale ya ce Ojougboh dan majalisar wakilai ne a shekarar 2003 zuwa 2007, kuma shugaban jam’iyyar APC ne a Delta.
Karanta wannan: Tsohon Ɗan Majalisar Wakilai ya rasu
NAN ta rawaito cewa marigayin ya mutu a lokacin da yake kallon wasan kusa da na karshe tsakanin Super Eagles da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu.
Hadimin shugaban kasar ya ce Tinubu ya jajantawa iyalan Ojougboh da gwamnati da al’ummar Delta bisa wannan rashi.
Ya ce Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma yi kira ga ‘yan uwa da su roka masa gafara a wajen Allah da kuma abubuwan tunawa da tarihin marigayin.