Iyalan marigayi Biliyaminu Bello sun bayyana rashin jin daɗinsu game da afuwar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bai wa Maryam Sanda, wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa bisa laifin kashe mijinta.
Iyalan sun bayyana matakin a matsayin babban zalunci da babu wani iyali da ya kamata ta fuskanci irinsa bayan rashin ɗan uwansu ta hanyar kisa.
A cikin wata sanarwa da Dr. Bello Mohammed ya fitar a madadin iyalan a ranar Litinin, sun ce matakin shugaban ƙasa na haɗa Maryam cikin jerin mutane 175 da aka yafewa a ƙarƙashin dokar bayar da afuwa, ya sake buɗe raunukan da suka fara warkewa a zuciyoyinsu.
Iyalan sun bayyana cewa Maryam Sanda, wadda kotun babbar birnin tarayya ta samu da laifin kashe mijinta a ranar 27 ga Janairu, 2020, ba ta nuna nadama ko sauyin hali ba tun daga lokacin da lamarin ya faru.
Labari mai alaƙa: Tinubu ya yafewa Maryam Sanda da wasu mutane 174
Sun kuma tuna cewa hukuncin kotun farko an tabbatar da shi ne ta kotun daukaka ƙara a ranar 4 ga Disamba, 2020, sannan kotun koli ta tabbatar da shi a ranar 27 ga Oktoban, 2023, abin da ya basu kwanciyar hankali cewa an samu adalci.
Sai dai sun bayyana cewa wannan sabon mataki na gwamnatin tarayya, bayan shekaru kaɗan da kisan ya faru, ya sake tayar musu da ciwon rai da suka fara mantawa da shi.
Iyalan sun bayyana takaici kan yadda gwamnati ta yi watsi da tsawon lokaci da aka ɗauka wajen shari’ar, tare da cewa an ba Maryam afuwa ne kawai saboda roƙon da iyalanta suka yi, ba tare da la’akari da raɗaɗin da iyalan mamacin ke ciki ba.
Sun ce wannan mataki ya tauye mutuncin marigayi Biliyaminu Bello kuma ya rage darajarsa kamar wani mutum da aka kashe kawai ba tare da adalci ba.
Iyalan sun kara da cewa laifin da Maryam ta aikata ya hana ‘ya’yanta samun soyayya da kulawar uba, duk da haka aka yi amfani da yaran wajen neman afuwa domin samun sassauci.
A ƙarshe, iyalan sun bayyana cewa sun bar lamarin ga Allah, Mai Shari’a na gaskiya, wanda zai yanke hukunci mai cikakken adalci a ranar sakamako.
Idan za a iya tunawa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da sakin mutane 175 daga gidajen yari a ƙasar nan a makon da ya gabata, bisa tsarin bayar da afuwa saboda dalilai na jin ƙai, ciki har da Maryam Sanda wadda aka yanke wa hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta Biliyaminu Bello a gidansu da ke Abuja a ranar 19 ga Nuwambar 2017.












































