Gwamna Mbah ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Peter Mbah

Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da sauya shekar sa daga jam’iyyar PDP zuwa APC).

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin jawabin sa ga jama’ar jihar a safiyar Talata, inda ya ce matakin nasa na da nufin haɗa jihar Enugu da gwamnatin tarayya domin samun cikakken haɗin kai da cigaba.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fifita ci gaban al’umma da walwala, kuma haɗin kai da gwamnatin tarayya zai taimaka wajen kawo cigaba mai ɗorewa ga jihar Enugu.

Gwamnan ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu bisa manufofinsa da suka kawo tallafi da ci gaba mai yawa ga Jihar Enugu tun bayan da ya hau mulki, yana mai cewa ba za su iya cigaba da zama gefe ba daga gwamnatin tarayya.

Sauya shekar gwamnan bai tsaya shi kaɗai ba, domin mambobin majalisar dokokin jihar, shugabannin ƙananan hukumomi, kansiloli, da sauran manyan ‘yan siyasa na jihar sun bi sahunsa.

Wannan mataki ya sake zama babban rauni ga jam’iyyar PDP a yankin Kudu maso Gabas, bayan jerin sauya shekar da dama da aka samu zuwa jam’iyyar APC a ‘yan watannin baya.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ma na shirin bin wannan hanya, yayin da a farkon shekarar nan, gwamnonin jihohin Delta da Akwa Ibom  Sheriff Oborevwori da Umo Eno suka koma jam’iyyar APC tare da tawagoginsu.

Masana harkokin siyasa na ganin wannan sauyi a matsayin sabuwar daidaita karfi a siyasar Kudu maso Gabas kafin zaɓen shekarar 2026.

Ana sa ran gudanar da babban taron tarbar gwamna Mbah a jam’iyyar APC a yau Talata a birnin Enugu, wanda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugaban jam’iyyar a ƙasa Netanwe Yitwalda, gwamnonin jam’iyyar da manyan jiga-jigai za su halarta.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here