Mahaifin Biliyaminu Bello da aka kashe, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya bayyana cewa ya amince da afuwar da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bai wa surukarsa, Maryam Sanda, inda ya ce ya dade da yafewa matar bisa laifin kisan da ta aikata ga ɗansa.
A lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, mahaifin marigayin ya ce ya karɓi afuwar shugaban ƙasa a matsayin “ƙaddarar Allah”, yana mai bayyana sakin Maryam a matsayin alamar jin ƙai da zai ba ta damar kula da ‘ya’yanta biyu.
Ya ce, shi musulmi ne kuma yana karɓar duk abin da ya fito daga Allah Madaukakin Sarki, inda ya ƙara da cewa ya yafe mata gaba ɗaya, ba tare da wata ƙiyayya ga gwamnatin tarayya ko danginta ba.
Ya kuma ce, ramuwar gayya ba za ta dawo da ɗansa ba, amma yafiya na iya kawo zaman lafiya.
Maryam Sanda, ‘yar tsohon babban jami’in kamfanin ajiya na Aso Savings, an same ta da laifin kisan mijinta, Biliyaminu Bello, wanda shi kuma ɗan uwa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta ƙasa, Alhaji Bello Haliru Mohammed.
Kotun babbar birnin tarayya ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya a watan Janairu na shekara ta 2020, bayan kisan da ya auku a watan Nuwamba 2017, wanda ya jawo fushi da mahawara a fadin ƙasar nan kan matsalar tashin hankali tsakanin ma’aurata da batun adalci.
Labari mai alaƙa: Yafewa Maryam Sanda da shugaba Tinubu ya yi babban zalunci ne – Iyalan marigayi Biliyaminu Bello
Alhaji Ahmed Bello Isa ya bayyana cewa roƙonsa na neman afuwa tun daga shekara ta 2019 ne, kafin ma kotu ta yanke hukuncin kisa.
Ya ce ya rubuta wasiku da dama zuwa hukumomi daban-daban, ciki har da tsohon babban lauya na tarayya Abubakar Malami da kwamishinan ‘yan sanda na birnin tarayya, yana neman sassauci ga surukarsa.
Sai dai a ranar Litinin wasu ‘yan uwa na marigayin karkashin jagorancin Dr Bello Mohammed sun fitar da wata sanarwa da ke soki afuwar, suna cewa wannan “babban zalunci ne da kowanne iyali ba zai so ya fuskanta ba.”
Amma da yake mayar da martani, Alhaji Ahmed Bello Isa ya nesanta kansa da wannan ra’ayi, yana mai cewa hakan ra’ayinsu ne, amma shi a matsayinsa na mahaifin marigayin ya zaɓi yafiya domin samun salama da rahamar Allah, da kuma domin rayuwar ‘ya’yan marigayin da mahaifiyarsu.













































