Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan yajin aikin gargadi na makonni biyu da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta ayyana, tana mai bayyana lamarin a matsayin barazana ga daidaiton tsarin ilimi na jami’o’i da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Wannan mataki ya biyo bayan wani muhimmin kudiri da dan majalisa Sesi Oluwaseun Whingan ya gabatar a ranar Talata, inda ya nemi gaggawar shiga tsakani ta majalisa domin kauce wa komawa cikin dogon yajin aiki kamar yadda ya faru a lokuta da dama a baya.
Whingan ya bayyana cewa yajin aikin ya samo asali ne daga matsalolin da ba a warware ba tsakanin ƙungiyar ASUU da gwamnatin tarayya, ciki har da aiwatar da yarjejeniyoyin baya kan kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, alawus na malaman jami’a, tsarin albashi, da ‘yancin cin gashin kai na jami’o’i.
Ya yi gargaɗi cewa duk da cewa wannan yajin aiki na yanzu na gargadi ne, irin waɗannan matakai a baya sun kan rikide zuwa dogayen rikice-rikice da ke lalata jadawalin karatu, kawo cikas ga bincike, da haifarda bacin rai ga ɗalibai.
Dan majalisar ya bayyana cewa tsarin jami’o’i na ƙasar nan ginshiƙi ne ga ci gaban tattalin arziki, fasaha, da bunƙasar ɗan Adam, don haka duk wata tangarda tana rage ƙarfin ƙasa wajen gogayya da sauran ƙasashe da kuma ingancin ilimi.
Karin labari: Gwamnatin tarayya ta umarci shugabannin jami’o’i su aiwatar da dokar “ba aiki, ba albashi” ga mambobin ASUU
Bayan tattaunawa, majalisar ta yanke shawarar umartar kwamiti na jami’o’i da na ma’aikata, aiki da samar da ɗamarar tattalin arziki, da su shiga tsakani nan take tsakanin ƙungiyar ASUU da gwamnatin tarayya domin samo mafita ta dindindin da za ta amfanar da bangarorin biyu.
Majalisar ta kuma yi kira ga duka ɓangarorin da su nuna haƙuri, su rungumi tattaunawa, su kuma sa muradun ɗalibai da ƙasa gaba a cikin kowane mataki da za su ɗauka.
Haka kuma, majalisar ta shawarci gwamnatin tarayya da ta kafa dandalin tattaunawa na dindindin da ƙungiyoyin jami’o’i domin tabbatar da ci gaba da sadarwa da gujewa yajin aiki a nan gaba.
An kuma umurci kwamiti na bin doka da tabbatar da aiwatar da matakai da ya kawo rahoto cikin mako guda kan yadda tattaunawar ke tafiya.











































