Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun sallah

Rauf Aregbesola. 2
Rauf Aregbesola. 2

Gwamnatin Najeriya ta ayyana Juma’a 21 da Litinin 24 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu a asar don gudanar da shagulgulan bukukuwan aramar sallah.

Ministan harkokin cikin gida na ƙasar Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hak a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan ya kuma taya al’ummar musulman ƙasar murnar kammala azumin wtan Ramadan.

Mista Aregbesola ya yi kira ga duka al’ummar musulmin ƙasar da su ci gba da ayyukan alkairin da suka koya a cikin watan na Ramadan.

Ya ce ”ina kira a gare ku da ku ci gaba da nuna wa juna halin dattaku, da soyayyar juna, da hakuri da juna da zaman lafiya da sadaukarwa da sauran kyawawan ayyuka, kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya koya mana”.

Ana sa ran gudanar da bikin ƙaramar sallah tsakanin ranar Juma’a da Asabar a Najeriya, yayin da ake daf da kammala azumin watan Ramadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here