Kar a siyasantar da matsalar tsaro; A mayar da hankali kan warware matsalolin Kano – Sanata Barau ga gwamna Abba

Barau Jibrin 3

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ya daina siyasantar da batun tsaro, ya kuma mai da hankali kan magance matsalolin da jihar ke fuskanta a halin yanzu.

Sanatan ya mayar da martani ne kan zargin da gwamnatin jihar ta yi cewa maganganunsa suna iya raunana kokarin tabbatar da tsaro a jihar bayan zaman majalisar zartarwa karo na 34 da gwamnan ya jagoranta.

Ya ce matsalolin tsaro da suka haɗa da shigar wasu yan ta’adda a sassan jihae na tayar da hankali na bukatar haɗin kai daga kowa domin magance su.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yada labarai, Malam Ismail Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya musanta zargin gwamnati, ya kuma kalubalance ta da ta fito da bidiyon da yake nuna cewa ya yi wata magana da za ta iya ƙara dagula tsaron jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi amfani da bayanan da ba su da tushe domin bata sunansa, lamarin da ya saba da ƙoƙarin da yake yi na haɗa kai da hukumomi domin magance matsalar tsaro a Kano da sauran sassan ƙasar.

Karanta: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta nemi a kama tsohon gwamna Abdullahi Ganduje

Sanatan, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma shine mataimakin shugaban majalisar ECOWAS na farko ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnan Kano za ta tashi tsaye wajen jagorantar harkokin gwamnati domin dawo da darajar da jihar ta yi suna da ita a baya.

Ya ce Kano ta taɓa zama kusa da Lagos wajen cigaba, amma barkewar matsalolin gudanar da mulki ya kawo koma baya, duk kuwa da cewa jihar na da duk abin da ake bukata domin komawa sahun gaba.

Sanarwar ta ce, domin inganta tsaro a jihar, Sanata Barau ya bayar da motocin aiki ga dukkan ofisoshin ‘yan sanda a mazabarsa da wasu sassan jihar, ya kuma bai wa dukkan jami’an ‘yan sanda a Kano ta Arewa babura domin taimaka musu a sintiri.

Haka kuma ya gyara wasu sassa na hedikwatar ‘yan sanda ta jihar tare da gina sababbin ofisoshin ‘yan sanda a wurare daban-daban, sannan ya bayar da irin wannan tallafi ga hukumar DSS a jihar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ya taimaka wajen kafa kwalejin horaswa ta hukumar NSCDC a Gwarzo, cibiyar horaswa ta hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda a Kabo da cibiyar hukumar shige da fice a Bichi, waɗanda duk ake ginawa a halin yanzu.

Yakuma saka fitilu masu amfani da hasken rana a dukkan mazabarsa da wasu sassan jihar domin sauƙaƙa sintirin dare, inda sanarwar ta ce gwamnatin jihar ya kamata ta yi koyi da irin wannan ƙoƙari maimakon yin zarge-zarge marasa tushe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here